Connect with us

Addini

Uwargidan Tinubu ta ba wa gwarzuwar Alƙur’ani kyautar Naira Miliyan 20

Uwargidan Shugaban Ƙasa, Oluremi Tinubu, ta bai wa Maryam Ibrahim Dan’Azumi kyautar N20m domin tallafa mata wajen karatunta, bayan da ta lashe gasar karatun Alƙur’ani ta ƙasa da ƙasa ta Sarki Abdulaziz da aka gudanar a Saudiyya.

An miƙa wa Maryam kuɗin ne a fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja ranar Talata, lokacin da Gwamnan Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, ya jagoranci tawaga domin gabatar da ita ga Uwargidan Shugaban Ƙasa. Gwamnan ya bayyana cewa ya yaba da irin tarbar da aka yi wa Maryam da kuma tallafin da aka ba ta.

Read Also : ADC ta zargi gwamnatin Tinubu da jefa ƴan Najeriya cikin ƙuncin rayuwa

Maryam, wadda ke karatu a makarantar Abubakar Siddiq Community School for Qur’anic Memorisation da ke Gombe, ta zama zakara a rukuni na biyu na gasar karo na 46 da aka gudanar a Makka, inda ta samu maki 97.70. Gasar ta kunshi haddar Alƙur’ani gaba ɗaya, karatu, Tajweed da tafsiri, kuma ita ce karon farko da aka ba mata damar shiga gasar cikin tarihin gasar.

Nasarar Maryam ta zo ne da kyautar da aka ruwaito ta kai N120m daga gasar Saudiyya. Haka kuma, ta taba lashe gasar karatun Alƙur’ani ta mata a matakin ƙasa a Maiduguri, yayin da ‘yar uwarta Hajara Ibrahim Dan-Azumi ta lashe gasar Alƙur’ani ta mata ta ƙasa da ƙasa a Jordan a shekarar 2024.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftdinamobetgrandpashabet girişgrandpashabetdinamobetGrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetDeneme Bonusu Veren SitelerCasibomcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasinolevantcasinolevantcasinolevantcasinolevantholiganbetjojobetgrandpashabetgrandpashabetsahabetsahabetonwinonwinmarsbahismatadorbetonwinsahabetsuperbetinmarsbahisjojobetgrandpashabetgrandpashabetholiganbettipobetsekabetsekabetholiganbetsahabetsahabetcasibomcasinolevantbetgarantibetciovdcasinosekabetmatbetimajbetcratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahissekabetgrandpashabetjojobetpusulabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabetGrandpashabet