Featured
Dangote na duba yiwuwar zuba $10bn domin magance matsalar wutar lantarki a Najeriya
Shugaban rukunin kamfanonin Dangote, Aliko Dangote, ya ce gamayyar kamfanoninsa na shirin zuba sama da dala biliyan 10 a fannin wutar lantarki domin taimakawa wajen magance matsalar rashin isasshiyar wuta a Najeriya da kuma bunƙasa masana’antu.
Dangote ya bayyana hakan ne a wata hira da gidan talabijin na Al Jazeera, inda ya ce sauye-sauyen manufofin gwamnati da rashin isasshiyar wutar lantarki na daga cikin manyan abubuwan da ke hana masu zuba jari saka kuɗaɗensu a Afirka. Ya ce ana iya karkatar da wasu kuɗaɗen da aka ware wa wasu harkokin kasuwanci, ciki har da ƙarafa, zuwa samar da wutar lantarki.
Read Also : Ɗariƙar Ƙadiriyya ta bayyana goyon bayanta ga Tinubu a zaɓen 2027
Ya kuma bayyana damuwarsa kan yadda sama da mutane miliyan 600 a Afirka ke ci gaba da rayuwa ba tare da samun wutar lantarki ba, yana mai cewa samar da wuta na da muhimmiyar rawa wajen bunƙasa tattalin arziki da samar da ayyukan yi. Dangote ya ce Afirka ba za ta iya samun ci gaba mai ɗorewa ba tare da bunƙasa masana’antu da rage dogaro da kayayyakin da ake shigowa da su daga ƙasashen waje ba.
Dangote ya kuma yi watsi da zarge-zargen cewa harkokin kasuwancinsa na haifar da babakere a wasu fannoni, yana mai cewa gwamnati ba ta ba kamfanoninsa wani haƙƙi na musamman na yin kasuwanci a kowane fanni ba. Ya ƙara da cewa zai ci gaba da saka hannun jari wajen sarrafa albarkatun Afirka a cikin nahiyar, domin ƙara musu daraja da kuma taimakawa wajen bunƙasa masana’antu.

Pingback: An yanke wa matashi hukuncin shekara guda a gidan gyaran hali kan satar tumatir - KAKAKI 24