Featured
Za mu dawo da tallafin man fetur bayan mun magance matsalar cin hanci da rashawa – Peter Obi
Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar NDC, Peter Obi, ya yi alkawarin cewa gwamnatinsa za ta dawo da tallafin man fetur idan aka zaɓe shi a zaɓen 2027, bayan ta magance matsalar cin hanci da rashawa a ƙasar.
Obi ya bayyana hakan ne a ranar Litinin a wani taron tattaunawa da aka shirya domin shi da ɗan takararsa na mataimakin shugaban ƙasa, Rabiu Musa Kwankwaso, a birnin Sokoto. Ya ce cin hanci da rashawa na daga cikin manyan ƙalubalen da ke addabar Najeriya.
Read Also : Talauci zai ƙara ta’azzara a Arewacin Najeriya matuƙar Tinubu ya faɗi zaɓe a 2027 – APC
Tsohon gwamnan Anambra ya ce idan aka magance cin hanci da rashawa, za a samu damar sake duba tsarin tallafin man fetur. Ya kuma ce gwamnatinsa za ta ɗauki matakan dakile cin hanci a dukkan ɓangarorin gwamnati domin a yi amfani da dukiyar ƙasa wajen inganta rayuwar jama’a.
Obi ya ce ilimi zai kasance ɗaya daga cikin manyan abubuwan da gwamnatinsa za ta bai wa muhimmanci bayan haɗin kan ƙasa da tsaro. Ya kuma yi alkawarin haɗa manyan biranen jihohi da layin dogo domin sauƙaƙa zirga-zirga da harkokin kasuwanci.

Pingback: YANZU-YANZU: Pantami ya lashe zaben fidda gwani na PDP a Gombe - KAKAKI 24