Featured
Ƙasashen Duniya Sun Yi Allah-wadai da Harin Houthi a Madina
Ƙasashe da dama sun yi kakkausar suka kan harin da ’yan Houthi suka kai wata tashar rarraba wutar lantarki a birnin Madina na Saudiyya, tare da bayyana goyon bayansu ga Saudiyya.
Turkiyya da Pakistan sun yi Allahwadai da harin, yayin da Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa, Bahrain, Kuwait da Jordan su ma suka yi tir da lamarin. Ƙungiyar Ƙasashen Larabawa da Ƙungiyar Haɗin Kan Musulunci sun bayyana harin a matsayin keta ’yancin Saudiyya.
Read Also : NNPCL ta ba wa matatun mai na Kaduna, Fatakwal da Warri rancen N220bn domin yin gyare gyare
Mai magana da yawun rundunar ƙawancen da Saudiyya ke jagoranta, Turki al-Maliki, ya ce harin ya lalata tashar rarraba wutar lantarki ta birnin. Ya ce bincike da ɓurɓushin jirgin mara matuƙi sun tabbatar da hannun ’yan Houthi wajen kai harin.
Al-Maliki ya ce harin ya sa ɗaya daga cikin na’urorin sauya ƙarfin wutar lantarki daina aiki, amma bai haifar da katsewar wutar lantarki mai yawa ba. Ya ƙara da cewa tashar ita ce ke samar da wutar lantarki ga Masallacin Annabi SAW.

Pingback: Ma’aikatan Gwamnati Sun Fara Yajin Aikin Kan Tsadar Rayuwa - KAKAKI 24