Connect with us

Featured

Borno : Kotu Ta Bayar da Belin Matasa 5 Da Aka Kama Sanye Da Rigar #TinubuMustGo

Wata kotun majistare da ke Maiduguri, jihar Borno, ta bayar da belin mutane biyar da aka kama ranar 25 ga Satumba bisa zargin sanya T-shirts masu ɗauke da rubutun #TinubuMustGo, lamarin da ya haifar da muhawara kan ’yancin faɗar albarkacin baki da siyasa.

Rundunar ’yan sandan Borno ta ce an samu kayayyaki da suka haɗa da nade-naden tabar wiwi 15, ƙwayoyi 100 da ake zargin D5 ne, butar shisha da almakashi, tare da T-shirts biyu masu rubutun #TinubuMustGo a hannun matasan. Sai dai rundunar ta musanta cewa an kama mutanen ne saboda ra’ayinsu na siyasa.

Read Also : Babban Sakataren Majalisar Ƙoli Kan Shari’ar Musulunci a Najeriya Ya Rasu 

Haka kuma, zargin da aka yi na cewa Gwamna Babagana Umara Zulum na da hannu wajen kamen ya jawo martani daga gwamnatin jihar. Gwamnatin ta ce gwamnan bai ambaci ƙungiyar #TinubuMustGo ko ADC ko wata ƙungiyar adawa ba, a yayin wata tattaunawa da manema labarai, illa batun tsaro, zaman lafiya da kare doka da oda.

Lauyan mutanen, Barista Alkali Askira, shugaban reshen Garki na ƙungiyar lauyoyin Nijeriya (NBA), ya tabbatar da cewa an bayar da belinsu. Ya kuma jaddada muhimmancin ’yancin faɗar albarkacin baki, amma ya shawarci matasa da su kasance masu bin doka tare da guje wa duk wani abu da zai iya jefa su cikin matsalar shari’a.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişGrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetBetwoonCratosroyalbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetcasibom xcasibom xgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasibomholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet