Featured
Ƙungiyar Ansaru ta dauki alhakin kisan Yahya Masussuka
Ƙungiyar Ansaru, wadda ake dangantawa da ƙungiyar Al-Qaeda, ta yi ikirarin kashe fitaccen malamin addinin Musulunci, Sheikh Yahaya Masussuka, ɗan jihar Katsina, tare da zarginsa da saɓa wa ƙa’idojin addini.
Ƙwararren mai sharhi kan harkokin tsaro, Audu Bulama Bukarti, ne ya wallafa bayanin ikirarin ƙungiyar a shafinsa na Facebook, inda ya ce ƙungiyar ta tabbatar da kisan ne ta wani saƙon murya.
Read Also : Gwamnan Kano Ya Yi Barazanar Korar Duk Jami’in Da Aka Kama Yana Sayar Da Kayan Tallafi
A cewar bayanin, ƙungiyar ta ce ta kai harin ne da misalin ƙarfe 8:30 na dare, sai dai ta yi kuskure wajen bayyana ranar da lamarin ya faru, inda ta ambaci Talata maimakon Litinin.
Rahoton ya kuma bayyana cewa ƙungiyar ta zargi marigayin da adawa da Musulunci, yayin da ake danganta matsayinsa na goyon bayan tattaunawa tsakanin mabiya addinai da zaman lafiya da dalilan da suka sa aka kai masa hari.

Pingback: Ƙishirwa ce ta yi sanadin mutuwar masu haƙar ma'adanai a Neja - Kwamitin bincike - KAKAKI 24