Featured
Mataimakin Sakataren Yaɗa Labaran NDC Na Ƙasa Ya Fice Daga Jam’iyyar
Mataimakin Sakataren Yaɗa Labarai na Ƙasa na jam’iyyar Nigeria Democratic Congress (NDC), Abdulmumin Abdulsalami, ya yi murabus daga jam’iyyar, bisa zargin rashin adalci, ware shi daga harkokin jam’iyyar da kuma tsoma bakin wasu manyan jami’ai.
Abdulsalami ya sanar da murabus ɗinsa ne a cikin wata wasiƙa da ya aikewa shugaban jam’iyyar na ƙasa, Sanata Moses Cleopas, ta hannun tsohon shugaban jam’iyyar na mazaɓarsa da ke Ƙaramar Hukumar Adavi a Jihar Kogi. Ya ce gudunmawar da yake bayarwa ta ci karo da muradun wasu manyan jami’an jam’iyyar.
Read Also : INEC Za Ta Bayyana Matsayarta Kan Rikicin ADC a Mako Mai Zuwa
Ya bayyana cewa ya yanke shawarar barin jam’iyyar ne domin samarwa kansa kwanciyar hankali, bayan korafe-korafen da ya ce ya sha yi kan rashin adalcin da ake masa. Ya kuma gode wa jagoran jam’iyyar, Sanata Seriake Dickson, da sauran waɗanda suka ba shi goyon baya a lokacin da yake aiki da jam’iyyar.
Sai dai kakakin yaɗa labaran jam’iyyar na ƙasa, Osa Director, ya musanta cewa akwai rikicin cikin gida a NDC, yana mai cewa ficewar mutum guda ba za ta nuna cewa jam’iyyar na cikin matsala ba.
