Connect with us

Labarai

Yadda al’umma su ka ƙwaci Sarkin Noma a hannun masu garkuwa da mutane a Kano

Ɗaruruwan mutane ne a garin Chiromawa da ke yankin ƙaramar hukumar Garun Malam a jihar Kano su ka ƙwaci ɗaya daga cikin masu riƙe da sarautar gargajiya da ke zaune a garin mai Alhaji Yusuf Nadabo, mai shekara 80 daga hannun masu garkuwa da mutane.

Alhaji Yusuf Nadabo wanda shi ne mamallakin gidan sayar da manfetur na Chiromawa Petroleum, haka kuma shi ke riƙe da sarautar Sarkin Noman Kano.

Tun da farko wasu rahotanni sun bayyana cewa ƴan ta’addar waɗanda su ka zo da ɗauke da muggan makamai domin yin garkuwa da Nadabo, sun dira a ofishin sa ne da ke Bakin Tasha da misalin ƙarfe 7:35, in da su ka riƙa harbi sama domin su razana jama’a.

Ai kuwa harbin nan na su bai razana al’umma ba, inda su ka tunkari ƴan ta’addar, har ma wani a cikin jama’ar garin ya samu raunuka na harsashi, kamar yadda wata majiya ta tabbatar.

“Ƴan ta’addar ba su samu nasara ba sabo da sun zo ne a ranar kasuwa. Akwai jama’a da dama ana ta hada-hada a yankin,” in ji shaidun gani da ido.

“Da su ka yi garkuwa da shi da ɗan sa Isyaku. Sai su ka yi tattaki zuwa maƙabarta inda su ka ɓoye baburan su. Amma ina, ai kuwa sai mutanen ƙauyen nan su ka dake, su ka bi su suna Kabbara.

“Bayan da harsashin ƴan ta’addar ya ƙare, shima kuma Alhaji Nadabo ba zai iya ci gaba da tafiya ba sabo da tsufa, sai su ka kwashe illahirin kuɗaɗen da ke aljihunsa, kimanin dubu 80, sai su ka ranta a na kare,” in ji majiyar.

Mai magana da yawun rundunar Ƴan Sanda ta Kano, Abdullahi Kiyawa, ya tabbatar da faruwar lamarin, in da ya ƙara da cewa sun samu nasarar kuɓutar da Sarkin Noman ne da haɗin gwiwa da al’ummar garin da kuma ƴan ƙato da gora na yankin.

“Mu na samun rahoton mu ka yi gaggawar tura jami’an mu wajen a daidai ƙarfe 7:57. Da haɗin gwiwar al’umma da ƴan ƙato da gora mu ka samu nasarar kuɓutar da Sarkin. Mu ka kuma daƙile yunƙurin yin garkuwa da shi,” in ji Kiyawa.

Share this:
meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetsweet bonanzacasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet