Connect with us

Labarai

Kaduna: Wasu Mafarauta Sun Kama Wani Ɗan Bindiga Tare Da Ceto Wasu Mutum 9 Da Akayi Garkuwa Dasu

Wasu mafarauta a kauyen Udawa da ke karamar hukumar Chikun a jihar Kaduna sun kama wani dan bindiga a wani daji da ke kan hanyar Kaduna-Birnin Gwari.

Mafarautan sun kuma kubutar da wasu mutanen kauyen guda 9 da aka yi garkuwa da su a farmakin da suka kai wa ‘yan bindigar da ke addabar yankin.

An tattaro cewa mafarautan sun yi wa barayin kwanton bauna ne kwanaki bayan da suka far wa ayarin matafiya a kan babbar hanyar.

Wani shugaban al’umma Muhammad Umaru ya shaida wa Daily trust cewa dukkan wadanda aka ceto daga kauyen Udawa ne.

“Aikin da mafarautanmu suka yi cikin nasara ne, domin sun yi nasarar ceto mutanen mu 9 daga hannun ‘yan bindigar, sannan kuma sun kama wani dan bindiga da ransa. Suna yi masa tambayoyi kafin su mika shi ga hukumomin tsaro,” inji shi.

An tattaro cewa mafarautan sun hadu da ‘yan bindigar wanda hakan ya tilastawa ‘yan bindigar barin wadanda abin ya shafa a sansaninsu.

Ya ce al’ummar yankin sun yi farin ciki da wannan nasarar da aka samu, inda ya ce idan aka tallafa wa mafarauta da ababen hawa, za su magance matsalar ‘yan bindiga a cikin al’umma da kauyukan da ke kewaye.

Shugaban al’ummar ya kuma yabawa jami’an tsaro da suka gudanar da wani samame a dajin bayan hare-haren biyu a jere a makon jiya.

Da aka tuntubi jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, ASP Jalige Mohammed, ya ce rundunar har yanzu ba ta karbi wani mutum da ake zargi daga wajen mafarautan ba, kuma ba a tuntube su kan lamarin ba.

Share this:
meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetsweet bonanzacasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetcasibomholiganbet xcasibomcasibomjojobetjojobetholiganbetholiganbetholiganbetholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabetjojobetjojobetgrandpashabetsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantjojobetcasibomgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet