Labarai
Bikin Salla: Sanata Barau ya buƙaci Musulmi su ci gaba da yin ayyukan alherin da suke yi a Ramadana
Shugaban kwamitin kula da kasafin kuɗi na majalisar dattawa kuma Sanata mai wakiltar mazaɓar Kano ta Arewa, Sanata Barau I. Jibrin, ya ja hankalin al’ummar musulmi da su ci gaba da gudanar da ayyukan alkhairai da suka koya a lokutan azumin watan Ramadana.
Barau Jibrin, ya bayyana hakan ne, ta cikin saƙonsa na Barka da Sallah da ya fitar a ranar Lahadi.
Ta cikin sanarwar ya ce, “Ya kamata Musulmi su yi ƙoƙari wajen kiyaye ayyukan alkhairan da suka gudanar a lokacin gudanar da azumi, tare da nisantar duk wata alfasha da suka ƙaurace wa musu a watan mai albarka.” inji shi.
Ya ƙara da cewa,” Bai kamata a yi ƙasa a gwiwa ba wajen nuna halayyar haƙuri da tsoron Allah da karamci da ƙaunar juna tare da yin riƙo da gaskiya da amana.”
Haka kuma ya ce, “Ya kamata mutane su ci gaba da bin koyarwar Annabi Muhammad Tsira da Aminci su tabbata a gare shi ta fuskar gaskiya da son zaman lafiya da kuma ƙaunar juna.”
Sanatan ya ce, ” Ta hanyar jin tsoron Allah ne kaɗai Musulmi za su iya yin fice da kuma samun nasara a dukkan al’amuran da suka sanya a gaba.
Sanata Barau, wanda kuma ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar gwamnan jihar Kano, ya kuma yi fatan masu hannu da shuni a Kano za su taimaka wa marasa ƙarfi da kayan abinci.”
Da yake martani kan zaɓen 2023, Sanata Barau ya buƙaci jama’a da su ƙara ƙoƙari wajen yin addu’o’in samun ingantaccen tsaro a Najeriya, wanda rashinsa zai iya haifar da matsaloli a harkokin zaben.
