Labarai
Gwamnatin Zamfara ta bada hutun mako guda domin yin katin zaɓe
Gwamnan jihar Zamfara, Bello Muhammad Matawalle, ya bai wa ma’aikatan gwamnatin jihar hutu na tsawon sati ɗaya domin su samu damar mallakar katin zaɓe.
Kwamishinan yaɗa labaran jihar Malam Ibrahim Magaji Dosara, ne ya sanar da hakan a ƙarshen makon nan ta cikin wata sanarwa da ya fitar.
Sanarwar ta ce “Mu na sanar da al’umma cewa mai girma gwamna Bello Matawalle Shatiman Sokoto, ya ayyana makon gobe daga ranar Litinin 20 ga Yuni zuwa ranar Juma’a 24 ga Yuni a matsayin ranakun hutu domin bai wa ma’aikata damar zuwa mazaɓunsu domin mallakar katin zaɓe watau PVC”.
Haka kuma sanarwa ta bai wa manyan jami’an gwamnati umarni da su ka haɗar da kwamishinoni da masu bada shawara na musamman da sarakunan gargajiya da sauran masu ruwa da tsaki da su sa ido kan yadda aikin yin rijistar zai gudana.
