Ilimi
Yajin Aiki: Ministan Kwadago Bai Gayyaci Kungiyar Mu Taro Ba —ASUU
Kungiyar Malaman Jami’o’i (ASUU) ta ce Ministan Kwadago da aiki yi Chris Ngige bai gayyaci kungiyar taro ba.
Ngige ya bayyana batun ne bayan taron majalisar zartarwa na tarayya a ranar Larabar da ta gabata ya ce zai gana da kungiyar domin ci gaba da tattaunawa kan yajin aikin da kungiyar ASUU ta shiga.
Sai dai shugaban ASUU, Emmanuel Osodeke ya ce ba a sanar da kungiyar ko wata ganawa da gwamnatin tarayya ba.
“Ba a gayyace mu zuwa wani taro ba. Babu daya daga cikin membobinmu da aka gayyata. Muna da sakatariya amma ba mu taba samun wata gayyata daga wurinsu ba,” in ji shugaban ASUU a wata hira da gidan talabijin na Channels ta cikin shirin Sunrise Daily a Alhamis din nan.
“Matsalar da muke da ita da wannan gwamnati, musamman na Ministan Kwadago, shi ne, idan za ka iya gaya wa duniya cewa ka shirya wani taro da ba ka yi ba, ta yaya za ka sa ran mu yarda da sauran abubuwan da ka fada?
“Ya kamata ya tabbatar wa duniya cewa ya aike da goron gayyata ga ASUU domin wani taro a ranar Alhamis.”
Farfesa Osodeke ya bukaci ministan kwadago da ya bar tattaunawa da kungiyar.
“Ya kamata ministan kwadago ya bar mu mu yi hulda da ministan ilimi. Shi ya kara dagula lamarin har haka,” inji shi.
“Shi ne ya yanke shawarar amfani da yunwa a matsayin makami lokacin da ya ce babu aiki babu albashi.”
ASUU, wacce ta fara yajin aikin na baya bayan nan tun ranar 14 ga watan Faburairu, ta yi nuni da rashin aiwatar da yarjejeniyoyin da gwamnati ta cimma da kungiyar.
A baya Ngige ya tabbatar wa ‘yan Najeriya cewa za a shawo kan matakin da aka dade nan ba da jimawa ba, yana mai cewa gwamnatin tarayya ta kuduri aniyar ganin an sake bude jami’o’in gwamnati.
