Uncategorized
Ƙungiyar ASUU ta buƙaci a yi dokar hana ƴan siyasa tura ƴaƴansu karatu ƙasashen ƙetare
Ƙungiyar malaman jami’o’i ta Najeriya ASUU, ta buƙaci da a yi dokar da za ta hana ƴan siyasa tura ƴaƴansu ƙasashen ƙetare domin yin karatu.
Shugaban ƙungiyar reshan jami’ar jihar Delta, Farfesa Kingdom Tombra, ne ya bayyana hakan yayin gudanar da zanga-zangar da ƙungiyar ƙwadago NLC ke yi domin mara wa ƙungiyar ASUU baya.
Ya ce, “Yin dokar zai bai wa jami’o’ in Najeriya dama su samu ci gaba da kuma samun ingantattun kayan aiki.
Haka kuma ya ƙara da cewa,” Ba wai ƙungiyoyin na yin Zanga-zangar ba ne don muzgunawa ƴan Najeriya, sai dai don ci gaban Najeriya da kuma bunƙasar ilimi.
Farfesa Kingdom Tombra, ya kuma ce,” Yin makaranta ɗaya a tsakanin ƴaƴan talakawa da na mahukuntan zai taimaka wajen magance matsalolin da ilimi ke fuskanta”.
