Connect with us

Labarai

Gwamnatin Jihar Gombe Ta Amince Da Tsawaitawa Wa’adin Kammala Wassu Hanyoyi

Gwamnatin Jihar Gombe Ta Amince Da Tsawaitawa Da Kammala Wassu Hanyoyi

Gwamnatin Jihar Gombe ta amince da tsawaitawa tare da kammala aikin wassu muhimman hanyoyi biyu na Ture zuwa Dogon Ruwa zuwa Gelengu, dana Ɓakasi zuwa Gelengu, wadda gwamnatin baya ta yi watsi dasu.

Kwamishinan Ayyuka da Sufuri na jihar Injiniya Abubakar Musa Bappa ne ya bayyana hakan ranar Larabar nan yayin wani taron manema labarai kan sakamakon zaman majalisar zartarwa ta jiha karo na 23 wadda Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya ya jagoranta a zauren majalisar zartaswa ta jiha dake gidan gwamnati.

Injiniya Bappa yace “Hanyar Ture zuwa Dogon Ruwa mai tsawon kilomita 23, gwamnatin data gabata ce ta bayar da aikin ta a 2013 kan kuɗi Naira biliyan 2 da miliyan 600 amma tayi watsi da ita saboda rashin biyan ‘yan kwangila, amma gwamnatin Muhammadu Inuwa Yahaya taga dacewar ƙarisa aikin tare da tsawaita hanyar da kimanin kilomita 19 zuwa Gelengu dake karamar hukumar Balanga bisa ƙarin kuɗi Naira biliyan 2 da miliyan 900”.

Kwamishinan yace shima aikin hanyar Ɓakasi zuwa Talasse da aka yi watsi da ita mai tsawon kusan kilomita 10 wacce ta hade ƙauyuka da dama za a kammala ta kan kudi Naira biliyan 2 da miliyan 600. Ya ce “Idan aka kammala aikin, hanyar zata bunƙasa harkokin noma da tattalin arziki da zamantakewar al’ummomin wannan yankin”.

Ya ƙara da cewa majalisar ta kuma amince da ɗaga darajar aikin titin Dukku zuwa Jamari mai tsawon kimanin kilomita 6 a Ƙaramar Hukumar Dukku kan kuɗi Naira miliyan 557.

Injiniya Abubakar Bappa yace ma’aikatar ta ziyarci wassu hanyoyi da dama da suka zagwanye sakamakon ruwan sama, inda wassu su ma suka yanke, yana mai cewa “gwamnatin jihar ta tantance yanayin lalacewar hanyoyin kuma ta fara ɗaukan matakan gyara”.

A nasa ɓangaren, Kwamishinan Kuɗi da Bunƙasa Tattalin Arziƙi na Jihar Muhammad Gambo Magaji, yace majalisar ta amince da tsarin kashe kuɗaɗen na matsakaicin zango daga 2023 zuwa 2025 don miƙawa Majalisar Dokokin Jiha tayi dubi tare da amincewa da shi.

Shima da yake nasa jawabin Kwamishinan Ilimi na Jihar Dauda Batari Zambuk, yace a yayin taron majalisar zartarwar karo na 23, Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya ya karɓi manyan lambobin yabo guda biyu; ɗaya daga Ma’aikatar Ilimi ta Tarayya bisa kasancewar Gombe jiha ta farko data samar da shafin yanar gizo kan tsarin kula da harkokin ilimi, da kuma samar da ingantattun bayanai game da yaran da basa zuwa makaranta, da kuma ƙoƙarin gwamnan na inganta fannin ilimi a jihar.

Yace lambar yabo ta biyu da gwamnan ya karɓa ita ce ta Gwarzon Gwamna na 2021 da Jaridar Vanguard ta ba shi, bisa ayyukan ci gaba da yake aiwatarwa masu nasaba ta kai tsaye da rayuwar al’ummar Jihar Gombe.

Kwamishinan dake sanya ido kan Ma’aikatar Yaɗa Labarai da Raya Al’adu ta Jihar kuma Kwamishinan Ilimi Mai Zurfi Mashak Audu Lauco ne ya jagoranci taron manema labaran.

JewelTimes

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetsweet bonanzacasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet