Labarai
Jami’an Yan Sanda Sun Kama Wasu Da Ake Zargin Da Hannu A Fashi Da Makami
Jami’an rundunar ‘yan sandan jihar Benue ta kama wasu mutane uku da ake zargi da hannu a fashi da makami da miyagun kwayoyi da kuma kasancewa mambobin kungiyoyin asiri.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, SP Catherine Anene, ce ta bayyana hakan a wata sanarwa da ta fitar ranar Laraba.
Anene ta bayyana cewa kamasu ya biyo bayan bayanan sirri da aka samu game da wasu gungun mutane uku da ke kai addabar al’umma a Wurukum, Bankin Arewa da kuma Kasuwar Zamani a Makurdi.
Ta ce, “Kwamishanan ‘yan sandan jihar Benue, Wale Abass, ya bayar da umarnin bin diddigin wadannan ‘yan fashi da makami a ranar 2 ga watan August 2022.
“An yi sa’a, a ranar 26/8/2022 da misalin karfe 1600 na safe, wadanda ake zargin: Fanen Wever, Philip Adanyi, wanda aka fi sani da Baron, da Albert Akor, wanda aka fi sani da J-Boy, dukkansu maza ne, wadanda ba su da wani takamaiman adireshi, an kama su ne a maboyar su dake Logo 1 na yankin Wurukum.”
Ta zayyana kayayyakin da aka kwato daga hannun wadanda ake zargin, wanda sun hada da bindiga guda daya da aka kera a cikin gida dauke da harsashi guda uku, da kullun ciyawa da ake zargin Tabar Wiwi ve, da sauran miyagun kwayoyi da kuma laya.
Anene ta kuma kara da cewa wadanda ake zargin sun amsa laifukan da ake zarginsu da shi.
