Labarai
Kano: Ƴan sanda sun tabbatar da mutuwar mutane 2 sakamakon harin ƴan bindiga daɗi
Rundunar ƴan sandan jihar Kano, ta tabbatar da mutuwar wasu mutane biyu sakamakon harbin su da wasu mutane ɗauke da bindigu suka yi.
Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar SP Abdullahi Haruna Kiyawa ne ya tabbatar da hakan ga jaridar Internet ta Solacebase yau Lahadi.
Ya ce tuni ƴan sanda suk fara gudanar da bincike kan kisan.
Da misalin ƙarfe 8:00 na daren jiya ne waɗanda ake zargin ƴan bindiga ne suka yi dirar mikiya tare da yin harbe-harbe a unguwar Sabon Gari da ke yankin ƙaramar hukumar Fagge.
Haka kuma jaridar ta ruwaito cewa, Wani ganau ya shaida mata wa ɓata garin sun isa wurin ne mai lamba 23 na a kan titin Neja ta hanyar Court Road inda suka fara harbin Ifeanyi Ilechukwu mai shekaru 41 wanda ya mutu nan take yayin da suka sake harbin Chibuke Emanuel mai shekaru 33 wanda ya cika a asibiti yayin da ake ba shi agajin gaggawa.
