Labarai
Fadar shugaban ƙasa ta musanta rahoton tsige shugaban INEC
Fadar shugaban ƙasa da ke Aso Villa a birnin tarayya Abuja, ta yi watsi da raɗe-raɗin da ake yaɗawa na cewa tana shirin tsige shugaban hukumar zabe mai zaman kanta INNEC, tare da yunƙurin dakatar da shirin yin amfani da tsarin na’urar zaɓe ta BVAS a babban zaɓen baɗi.
Mai magana da yawun fadar shugaban kasar Mista Femi Adesina ya bayyana hakan a wani shirin tattaunawa kan manufofin da aka shirya domin tunawa da ranar kawo karshen cin zarafin ƴan jarida ta duniya na bana wanda aka gudanar a Abuja.
Jaridar Solacebase ta ruwaito cewa Adesina, ya kuma shawarci manema labarai da kada su biyewa masu aniyar kawo cikas a zaɓen na baɗi ta hanyar yaɗa jita-jita.
“A kwanan nan, akwai wata ƙungiya da ta ce akwai alamun za a tsige shugaban hukumar INEC saboda kila ba sa son amfani da na’urar BVAS mai daƙile duk wata hanyar magudi.
“ Sai da fasaha ta zo aka samu katin zabe na dindindin don haka abu ne mai wuya a rubuta sakamako.
Femi Adesina ya ƙara da cewa a ranar Litinin din da ta gabata ne shugaba Buhari a wani taro a jihar Imo, ya kuma baiwa ‘yan sanda umarnin tabbatar da zaben 2023 cewa zai zamo mai inganci.
