Labarai
Shugaban jam’iyyar PDP na Zamfara ya rasu
Jam’iyyar adawa ta PDP a jihar Zamfara ta sanar da rasuwar shugabanta Dakta Ahmed Sani Ƙaura.
Sakataren jam’iyyar Faruk Ahmed Gusau, ne ya bayyana hakan ga manema labarai, yana mai cewa marigayin ya rasu ne bayan ganawa da majalisar malamai ta jihar.
Haka kuma ya ce, tun da fari, Majalisar malaman ce ta gayyace shi domin tattaunawa kan yadda za a shawo kan matsalar dabanci a yaƙin neman zaɓen baɗi.
Faruk Ahmed Gusau, ya ƙara da cewa jim kaɗan bayan kammala taron ne shugaban jam’iyyar ya faɗi, kuma bayan kai shi asibiti likitoci suka tabbatar da rasuwarsa.
