Featured
Kachallan Kutumbawa Ya Taya Sarakunan Kano Da Bichi Murnar Samun Lambar Girma
Kachallan Kutumbawan Kano Alhaji Dahiru Muhammad Maihula ya aike da sakon murna ga Mai Martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero bisa lambar girma ta CFR wadda shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ba shi.
Kachallan na Kutumbawa yace hakika Mai Martaba Sarkin na Kano ya cancanci wannan lambar girma, bisa la’akari da hidimar sa ga al’umma da kuma gudummawar sa ga hadin kan kasa.
Haka kuma Kachalla Kutumbawa ya taya Sarkin Bichi murnar samun lambar girma Alh. Nasiru Ado Bayero Ganin yacce yake hidimtawa Addinin musulunci a ciki da wajen kasar nan. Inda ya ce Sarkin Bichi yana koyi irin na marigayi Sarkin Kano Ado Bayero wajen zumunci da taimakon talakawa.
Wata sanarwa da aka rabawa manema labarai dauke da sa hannun sa, Kachalla yace bayyana Aminu Ado Bayero a matsayin adalin Sarki, mai hakuri da dattaku tamkar mahaifinsa marigayi Alhaji Ado Bayero.
Dahiru Muhammad Maihula ya yabawa shugaban kasa Muhammadu Buhari bisa bada lambar girma ga sarkin na Kano.
Sannan ya yi addu’ar fatan alheri ga jihar Kano da Najeriya Baki Daya, tare da fatan gudanar da zabukan Shekara Mai zuwa cikin lumana.
