Labarai
Shugaba Buhari ya gana da Sarki Charles III
Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, ya gana da sabon sarkin Ingila Charles III, a fadar Buckingham da ke birnin London.
Mai taimaka wa shugaba Buhari, kan kafafen sada zumunta na intanet Bashir Ahmad ya bayyana hakan ta cikin wani saƙo da ya wallafa tare da hotunan ganawar ta su a shafinsa na Twitter.
Sai dai Bashir Ahmad bai yi bayani kan tattaunawar da ta wakana tsakanin shugabannin ba.
Rahotonni sun bayyana cewa wannan ce ganawa ta farko tsakanin shugaba Muhammadu Buhari da Sarki Charles tun bayan hawan sarkin na Ingila kan karagar mulki.

binance us registrace
23/02/2024 at 7:47 pm
Thanks for sharing. I read many of your blog posts, cool, your blog is very good. https://accounts.binance.com/cs/register-person?ref=IQY5TET4