Labarai
Wata Gobara Ta Tashi A Shedikwatar Yan Sanda Ta Jihar Kano
Gobara ta tashi ta kone shedikwatar ‘yan sandan Kano, da ke Bompai da yammacin ranar Asabar din nan.
Jaridar Alkiblah ta tattaro cewa gobarar ta tashi ne daga ofishin Provost ta kuma bazu zuwa sashen kudi, dakin taro, ofishin PPRO, ofishin mataimakin kwamishinan (Admin), ofishin mataimakin kwamishinan (Admin) da dai sauransu.
An tattaro cewa dukkan ofisoshin da ke saman benen ginin na tun shekarar 1967 gobara ta kone su, sai ofishin kwamishinan.
“Mun yi kokarin kashe gobarar ta ofishin Provost da ta tashi ta hanyar amfani da na’urar hannu amma sai wutar ta bazu zuwa wasu ofisoshin.
“‘Yan kwana-kwana wato jami’an hukumar kashe gobara sun isa wurin ne kusan sa’o’i 2 bayan tashin gobarar,” wata majiya ta shaida wa DAILY NIGERIAN.
