Connect with us

Labarai

Kotu ta bada umarnin tsare Murja Kunya a gidan Yari

Wata Kotu a jihar Kano, ta bayar da umarnin tsare fitacciyar ƴar TikTok Murja Ibrahim Kunya, a gidan Gyaran Hali.

Kotun ta  bada umarnin ne da tsakar ranar yau Alhamis bayan da ta kammala sauraron shari’ar da ake yi wa Murja Ibrahim, inda ta ce a ci gaba da tsare ta zuwa ranar  16   ga  wannan watan da muke ciki na Faburairu da za a dawo domin ci gaba da shari’ar.

Ana zargin Murja Ibrahim Kunya, da yin kalaman rashin  ɗa a  da suka  saɓa da tarbiyya har ma  zamantakewar musulmi.

Tun farko dai Zauren haɗin kan malaman jihar Kano ne  suka yi ƙarar matashiyar da wasu sauran matasa maza da mata a Kotun shari’ar musulunci da ke garin Bichi, inda a cikin makon da muka yi ban kwana da shi ƴan sanda  suka  cafke ta.

Sai dai, bayan karanta mata tuhume-tuhume Murja Ibrahim ta musanta batun.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişGrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetBetwoonCratosroyalbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahisgrandpashabetcasibom xcasibom xgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasibomholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet