Featured
Wani Mutum Ya Rasa Ransa A Layin Cirar Kuɗi A Banki
Wani mutum ya yanke jiki ya faɗi yayin da yake tsaka da bin layin cirar kudi a wani banki a Karamar Hukumar Ika ta Kudu a Jihar Delta.
Rahotanni sun tabbatar da cewa mutumin ya shafe sa’o’i yana bin layin cirar kudi a na’urar ATM yayin da ƙarar kwana ta cim masa.
Jami’in Hulda da jama’a na Rundunar ’Yan sandan Jihar Delta, DSP Bright Edafe ne ya tabbatar da faruwar lamarin.
A cewar DSP Edafe, “mutumin wanda ya daɗe a kan layi domin cirar kuɗi ya zo ne domin karbar katinsa na ATM.”
A halin yanzu dai al’ummar Najeriya na ci gaba da gunaguni dangane da ƙarancin sabbin takardun Naira da aka sauyawa fasali, la’akari da yadda wa’adin karɓar tsohuwar Nairar ya ƙarato.
A ranar Lahadin da ta gabata ne Babban Bankin Najeriya CBN ya tsawaita wa’adin amfani da tsohuwar naira da kwanaki goma.
A cewar Babban Bankin, wa’adin karbar tsohuwar Nairar zai cika a ranar 10 ga watan Fabrairu, wanda kuma Gwamnan na CBN, Godwin Emefiele ya ce babu gudu babu ja da baya.
Aminiya ta ruwaito yadda zanga-zanga ta barke a jihohin Oyo da Delta dangane da yadda jama’a ke ci gaba tagayyara saboda karancin sabbin takardun kuɗaɗen a hannun jama’a.
