Labarai
Shugaba Buhari Ya Gana Da Gwamnan CBN Bayan Umarnin Kotun Koli
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya gana da Godwin Emefiele, gwamnan babban bankin Kasa (CBN), a fadar shugaban kasa, a sirri.
A ranar Larabar nan ne dai kotun koli ta dakatar da gwamnatin tarayya na wani dan lokaci daga hana amfani da tsoffin kudaden naira daga ranar 10 ga watan Fabrairun da muke ciki.
Sai dai har yanzu ba a san sakamakon taron ba.
Kwamitin Alkalai mai mutum bakwai na Kotun Koli karkashin jagorancin Mai Shari’a John Okoro, a cikin wani hukunci daya yanke, ya amince da hukuncin na wucin gadi bayan gwamnatocin jihohin Kogi, Kaduna da Zamfara suka shigar da kara a kai.
Kotun kolin ta kuma bayyana cewa gwamnatin tarayya da babban bankin CBN su dakata har sai an yanke hukunci a ranar 15 ga watan Fabrairu.
Jaridar SOLACEBACE ta rawaito cewa Har yanzu dai ba a san sakamakon taron ba amma ziyarar ta shugaban bankin na da alaka da hukuncin kotun koli.
