Kasuwanci
CBN ya musanta raɗe-raɗin katse hanyoyin tura kuɗi ta Internet saboda zaɓe
Babban bankin Najeriya CBN, ya musanta raɗe-raɗin da ake yaɗawa cewa zai katse hanyoyin tura kuɗi ta Internet saboda kusantowar babban zaɓen bana.
CBN ya musanta batun ne ta cikin wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na Twitter a Larabar makon nan yana mai cewa labarin wanda ake yaɗawa a kafafen sada zumunta na ƙanzon kurege ne.
Tun a farkon makon nan ne labarin ya karaɗe shafukan sada zumunta na zamani, lamarin da ya jefa fargaba a zukatan al’umma.
Haka zalika wannan jita-jita ta sanya wasu cikin ƴan Najeriya fara samar wa kansu matakan ko ta kwana la’akari da irin matsalar da suke ganin katse hada-hadar za ta janyo matuƙar ta tabbata.
