Featured
NNPP ta zargi shugaban jam’iyyar APC da yiwa ɗan takararta rashin kyautawa
Jam’iyar NNPP ta bayyana rashin jin dadin ta, bisa yadda wasu ɓata gari suka farwa dan takarar gwamnan jahar Kano Eng. Abba Kabir Yusuf a mazabarsa dake Chiranci a karamar hukumar Gwale.
Jam’iyyar ta zargi shugaban jam’iyar APC na jahar Kano Abdullahi Abbas, da wasu yan barandar siyasa ne suka afka masa tare da rera wakokin tunzura al’umma da kuma jifa da Duwatsu.
Cikin wata sanarwa da mai magana da yawun dan takarar Sanusi Bature Dawakin Tofa ya rabawa manema labarai, ya ce babu wanda ya samu rauni a cikin tawagar ɗan takarar gwamnan.
