Labarai
Bayan shafe kwanaki 18: Shugaba Buhari ya koma fadar Villa
Bayan shafe kwanaki 18 ba ya nan, Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, ya koma fadar mulki watau Aso Villa da ke birnin tarayya Abuja.
Mai magana da yawunsa Malam Garba Shehu, ne ya sanar da komawar tasa ta cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa ta Twitter da tsakar ranar yau Litinin.
Sanarwar ta Malam Garba Shehu, ta ce shugaba Buhari ya koma Abuja ne bayan kwanaki 18 tun bayan da ya yi zaɓen shugaban ƙasa a mahaifarsa Daura a jihar Katsina.
Haka kuma saƙon ya bayyana cewa bayan nan shugaban ya kai ziyara Maidugurin jihar Borno tare da halartar taron Majalisar Dinkin Duniya a birnin Doha na ƙasar Qatar.
