Connect with us

Featured

TRT ta ƙaddamar da sashen Hausa da wasu harsuna 3

Kafar yaɗa labarai ta ƙasar Turkiyya wato TRT ta ƙaddamar da ƙarin bangarori guda uku da za su dinga yaɗa labarai cikin harshen Hausa da Swahili da Turanci da kuma Faransanci.

Tashar ta TRT ta yaɗa taron masu ruwa da tsaki a harkar na nahiyar Afrika da aka gudanar a yau juma’a a birnin Istanbul da ke ƙasar ta Turkiyya.

Tun da farko an kaddamar da tashar wacce za ta dinga kawo labarai da rahotanni bisa tsarin dokar yaɗa labarai a gaban mambobin kungiyar watsa labarai na nahiyar Afirka da manyan jami’an gwamnati da kuma jami’an diflomasiyya.

“TRT Afrika za ta kasance kafar yaɗa da za ta dinga bayyana gaskiya da hakikanin zahirin nahiyar Afirka. Wannan dalilin ne ya sa takenmu ya kasance “Afrika a zahiri” a cewar Darakta Janar na TRT, Mehmet Zahid Sobaci.

Ya ƙara da cewa manyan an kwashe tsawon lokaci akan yadda kafafen yaɗa labarai na duniya ba sa kawo rahotanni akan kyawawan al’adun nahiyar Afirka da dabi’u da kuma rahotanni masu fa’ida. Sai dai kawai sun ɓige da yaɗa manufofin kafofin yaɗa labarai na yammacin duniya.

“Idan muka kalli Afirka, za mu tabbatar da cewa tana da kyakkyawar makoma” in ji shi.

Har ila yau, kafar yaɗa labaran za ta zama wata muryar labaran Afirka da ‘yan Afirka a kasashen waje, tare da samar da wani dandali na musamman da zai bayyana ainihin dabi’un al’ummar nahiyar Afrika a cikin abubuwan da ke faruwa a fadin duniya.

A ƙarshe ya ce babban muradin tashar TRT Afrika da ta ke da ma’aikata guda 15 daga kasashe daban daban shi ne samar da ingantattun labarai na musamman tare da yada su cikin fasahar zamani da kuma gabatar da shirye-shiryen da su ka shafi rayuwar al’ummar Afirka da su ke zaune a ko ina a fadin duniya.

Share this:
meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişGrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetBetwoonCratosroyalbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahisgrandpashabetcasibom xcasibom xgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasibomholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet