Labarai
Wata Kotu Ta Daure Wani Matashi Da Ta Samu Da Laifin Satar Inji
Wata kotun majistare da ke Kaduna a ranar Talatar nan ta yanke wa wani matashi mai suna Bala Hassan mai shekaru 25 hukuncin daurin watanni 10 a gidan yari.
Matashin an yanke masa hukunci ne bisa samunsa da laifin hada baki da satar injin janareta da ya kai Naira 450,000.
Wanda aka samu da laifin a Ungwan Dosa, dake Kaduna, ya amsa laifin da ake tuhumarsa da shi, ya kuma roki kotu da ta yi masa sassauci.
Da yake yanke hukunci, Alkalin kotun, Mista Ibrahim Emmanuel, ya ce wanda ake kara ana yanke masa hukunci ne bisa ga amsa laifinsa.
“Kotu ta samu wanda ake tuhuma da aikata laifin, a daidai lokacin da ya roki sassauci, wanda shi ne wanda ya aikata laifin a karon farko, wanda bai batawa kotu lokaci ba.
“An yankewa Bala Hassan hukuncin daurin watanni 10 a gidan yari tare da zabin biyan tarar Naira 20,000, inji alkalin kotun.
Ya ce hukuncin zai zama katanga ga masu son aikata duk wani laifi.
Emmanuel, ya umarci wanda aka yankewa hukuncin da ya biya diyyar Naira 450,000 ga wanda ya kai karar Mohammed Danladi.
Tun da farko, lauyan masu shigar da kara, Chidi Leo, ya shaida wa kotun cewa a ranar 23 ga watan Yuni, Hassan da wani daga cikinsu, sun hada baki tare da sace wani janareta wanda kudinsa ya kai Naira 450,000 mallakin wanda ya kai karar a Badarawa Kaduna.
Leo ya ce yayin binciken ‘yan sanda, wanda ake kara ya amince da aikata laifin; sai dai duk kokarin da aka yi na dawo da janareta lamarin ya ci tura.
Leo ya ce laifukan sun ci karo da sashi na 302 da na 217 na kundin laifuffuka na jihar Kaduna na shekarar 2017. (NAN)
