Connect with us

Featured

‘Yan Sanda Sun Kama Wasu Mutane Biyu Da Ake Zargin Barayin Mota Ne

Rundunar ‘yan sandan Najeriya reshen jihar Nasarawa ta cafke wasu mutane biyu da ake zargi da satar mota a karamar hukumar Lafiya ta jihar.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, DSP Ramhan Nansel, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya rabawa manema labarai a Lafia ranar Lahadi.

Ya bayyana cewa bayan sun sace motar, wadanda ake zargin masu shekaru 49 da 38 ne, sun tsere zuwa jihohin Taraba da Filato, amma an kama su ne bayan da jami’an ‘yan sandan suka yi kokarin kama su.

Ya ce, “A ranar 19 ga watan Yulin 2023 da misalin karfe 4 na yamma, an shigar da kara a ofishin ‘yan sanda na ‘B’ Dibision dake Lafia cewa an baiwa wani bakaniki mota kirar Toyota Corolla, 2015 a Lafia domin ya gyara.

“Duk da haka, wanda ya aikata laifin ya tafi da motar zuwa wurin da ba’a sani ba, kuma duk kokarin da aka yi na isa wurinsa ya ci tura.

“Sakamakon korafin, jami’an ‘yan sandan da ke aiki a sashin ‘B’, Lafiya sun gudanar da bincike mai zurfi kan lamarin.

“Saboda haka, babban wanda ake zargin, Sani Musa Labaran ‘M’ mai shekaru 49 ma zaunin hanyar Shinge dake Lafiya, an kama shi a Gembu, jihar Taraba, yayin da aka kama abokin aikinsa, Ibeto Nwobodo ‘M’ mai shekaru 38 a Faringada, Jos.

“Da aka yi musu tambayoyi, wadanda ake zargin sun amsa cewa sun hada baki ne wajen siyar da motar kan tsabar kudi Naira miliyan 2.5.

Nansel ya kara da cewa kwamishinan ‘yan sanda, Maiyaki Baba ya yaba wa jami’an bisa yadda suka gudanar da aiki mai kyau. Sannan kuma ya ba da umarnin gurfanar da wadanda ake zargin zuwa kotu domin girbar abinda suka shuka.

Share this:
meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetsweet bonanzacasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet