Ilimi
Kano: Jami’ar BUK Ta Bullo Da Wani Shirin Samar Wa Dalibai Aikin Yi
Shugaban jami’ar Bayero ta Kano (BUK), Farfesa Sagir Adamu Abbas, ya bayyana cewa makarantar ta bullo da tsarin samar da aikin yi ga dalibai.
Adamu Abbas ya ce jami’ar ta dauki nauyin dalibai don gudanar da wasu ayyuka a makarantar, kuma suna biyan dubu N15,000 duk wata.
Ya yi wannan jawabi ne a karshen makon da ya gabata a Kano lokacin da ya karbi bakuncin tawagar kungiyar masu aiko da rahotanni ta kasa (ECAN) a babban harabar jami’ar.
Adamu-Sagir ya ce: “Jami’ar ma ta bullo da wani nau’in tsarin yi wa dalibai aikin yi, inda suka dau nauyin yin wasu ayyuka a jami’ar kuma ana biyan su Naira 15,000 duk wata.
“Wannan bai shafi karatunsu na yau da kullun ba saboda ba ya ɗaukar lokaci mai yawa kamar yadda wasu za su share wasu kewaye ko yin wani aiki a jami’ar kuma ana biyan su a ƙarshen wata.”
Da yake magana kan karin kudin rijistar, mataimakin shugaban jami’ar ya koka kan yadda ake kashe kudaden gudanar da wannan jami’a, musamman abinda ya shafi tsadar samar da wutar lantarki.
Ya bayyana cewa kudin wutar lantarkin ya kai kusan Naira miliyan 35 duk wata, yayin da kudin sayen dizal na janareta ya kai kimanin Naira miliyan 40.
Shugaban jami’ar Adamu-Abbas ya ce dole ne jami’ar ta kara yawan kuɗin rijista, saboda a zahiri abu ne mai wuya a samar da ayyukan jin dadin jama’a ga dalibai kusan 45,000 da suka hada da wadanda suka kammala karatun digiri, da ma’aikata sama da 5,000, na koyarwa da wanda basa koyarwa.
