Connect with us

Tsaro

Hukumar NYSC Ta Gargadi ‘Yan Bindigar Da Suka Sace Mambobinta – DG

Darakta Janar na Hukumar Kula da Masu yi wa Kasa hidima ta Kasa, Burgediya Janar Yush’au Ahmed, a ranar Alhamis, ya ce hukumar gudanarwar shirin na yin namijin kokari wajen ganin an sako wasu sauran mambobin hukumar NYSC biyar da aka sace kwanan nan a jihar Zamfara.

Shugaban ya bayyana hakan ne a lokacin da ya bayyana tare da tawagarsa a gaban kwamitin majalisar wakilai kan ci gaban hukumar ta NYSC.

Ya kuma jaddada cewa, don ganin an sako mambobin, tuni hukumomin tsaron da abin ya shafa ke hada kai da hukumomin gargajiya da na addini.

A cewarsa, an kubutar da uku daga cikin mutane takwas da aka yi garkuwa da su a watan Agustan 2023 yayin da suke tafiya sansanin masu yi wa kasa hidima na NYSC a jihar Sokoto. Tuni dai aka mayar da mambobin zuwa babban birnin tarayya Abuja, bayan samun kulawar da ta dace.

Ahmed ya ce, “Muna kokarin ganin mun fitar da yaran daga hannun wadanda sukw tsare da su. Muna tuntuɓar ‘yan bindigar. Daga dukkan alamu da muke samu, muna fatan za mu same su da nan ba da jimawa ba.”

DG ya yi gargadi kan yin tafiye-tafiye da daddare, yana mai jaddada cewa hakan ya saba wa shawarar tsaro da hukumar ta bayar ga daukacin ‘yan NYSC da masu son shiga.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişGrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetDeneme Bonusu Veren SitelerCratosroyalbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasinolevantjojobetgrandpashabetmarsbahismarsbahismarsbahisjojobetjojobetjojobetjojobet girişmarsbahisjojobetgrandpashabetholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabet girişjojobetjojobetgrandpashabetsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahisjojobetjojobetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet