Connect with us

Labarai

Gwamnatin Tarayya Ta Dakatar Da Shirin N-power Sai Abun Da Hali Ya Yi

Gwamnatin tarayya ta sanar da dakatar da shirin nan na tallafawa matasa da aka fi sani da N-Power har abada.

Ministar harkokin jin kai da kula da bala’o’i Betta Edu ce ta bayyana hakan yayin da take jawabi a wani shirin gidan talabijin na TVC ranar Asabar din nan.

Ta ce an dauki matakin ne sakamakon wasu kura-kurai a cikin shirin, inda ta ce gwamnati ta kaddamar da bincike kan yadda aka yi amfani da kudaden tun bayan fara shirin.

Ministar ta yi ikirarin cewa ba a samun wasu daga cikin wadanda suka ci gajiyar tallafin a wuraren ayyukansu amma suna tsammanin biyan alawus na wata-wata.

A cewarta, ya kamata wasu daga cikin wadanda suka ci gajiyar shirin su fice daga shirin tun 2022 amma har yanzu suna kan samun albashi.

Ta ce, “Dole ne mu koma mu duba N-Power mu fahimci mene ne matsalolin don haka za mu dakatar da shirin a yanzu har sai an kammala binciken da ya dace kan yadda ake amfani da kudade a cikin shirin na N-Power.

“Muna so mu san mutane nawa ne a cikin shirin a yanzu, mutum nawa ake bi bashi, adadin da ake bin su. Muna sake fasalin N-Power gaba daya tare da fadada shi.

“Akwai abubuwa da yawa da ke faruwa. Mun sadu da mutanen da ya kamata su bar shirin tun bara kuma har yanzu suna ci gaba da ikirarin cewa har yanzu suna koyarwa.

“Wani lokaci muna tuntuɓar makarantar ko wuraren da suke aiki kuma ba sa nan. Ba sa aiki har yanzu suna ci gaba da ikirarin cewa suna bin alawus alawus na watanni takwas ko tara.

“Kusan kashi 80 cikin 100 na su ba sa aiki tukuna suna neman albashi”.

Jaridar DAILY POST ta ruwaito cewa gwamnatin tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ce ta bullo da shirin na N-Power domin magance matsalar rashin aikin yi ga matasa don taimakawa ci gaban al’umma.

Share this:
1 Comment

1 Comment

  1. Pingback: Kaduna: ‘Yan Sanda Sun Kama Wasu Mutum 10 Bisa Zargin Masu Garkuwa Da Mutane Ne - KAKAKI HAUSA

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişGrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetBetwoonCratosroyalbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahisgrandpashabetcasibom xcasibom xgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasibomholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet