Connect with us

Tsaro

Yadda ‘Yan Sanda Neja Suka Kama Wani Da Aka Zargi Da Kisan Kai

 

Rundunar ‘yan sandan jihar Neja ta bayyana yadda ta kama wani mutum da ake zargi da kisan kai mai suna Usman Yahaya Muhammad daga kauyen Kinboku-Kudu da ke karamar hukumar Mokwa a jihar.

Rundunar ta yi zargin cewa wanda ake zargi da kisan gillar ya kashe wani direban babur.

Da yake jawabi a yayin holan Muhammad da sauran wadanda ake zargin a Minna, babban birnin jihar, jami’in hulda da jama’a na rundunar a jihar, DSP Wasiu Abiodun, ya tabbatar da kamun.

Inda ya bayyana cewa bayan kashe direban wanda ake zargin ya jefar da gawar ya gudu da babur din daga wurin.

A halin da ake ciki, Mohammad ya amince da aikata laifin a wata hira da aka yi da shi, inda ya bayyana cewa ya hau babur din wanda ya kashe ya nufi kauyen Eppa. Sai dai kafin ya isa inda ya nufa ya kashe mai babur din.

Da aka tambaye shi dalilin kisan, ya ce, “Ba zan iya cewa ga dalilin da ya sa na kashe shi ba. Ko Wwani abu da ya sa na yi ba. Bayan na kashe shi, sai na kai rahoton kaina ga shugaban ‘yan banga da ke yankinmu, wanda daga nan ne ya kai rahoto ga ‘yan sanda lamarin da ya sa aka kama Ni.”

“Na shake mai Okadar har ya mutu a wuya sau biyu, sai ya fadi. Sai na tafi da babur din.”

Da aka tambaye shi ko yana so ya fuskanci irin wannan kaddara da abin da ya yi wa wanda aka kashe, sai ya ce, “A’a, ina so in mutu kamar yadda ake mutuwa. Ina so in rayu.”

Wanda ake zargin ya kuma bayyana cewa ranar Juma’a ne aka shirya daurin aurensa kuma ya taba aikata irin wadannan laifuka sau takwas.

Rundunar ‘yan sandan ta kuma bayyana cewa, a baya-bayan nan ta kama wasu mutane 38 da ake zargi, 7 daga cikinsu an gurfanar da su a gaban kotu bisa laifuka daban-daban da suka hada da fashi da makami, da garkuwa da mutane, da fashi da makami, da kisan kai da dai sauransu a jihar.

Share this:
1 Comment

1 Comment

  1. Pingback: Gwamnatin Tarayya Ta Bayyana Adadin Da Suka Mutu A Watanni 10 Sanadin Mashako - KAKAKI HAUSA

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet