Featured
Sokoto: Wasu Da Ake Kyautata Zaton ‘Yan Bindiga Ne Sun Hallaka Mutane 11
Akalla mutane 11 ne wasu ta’adda da ake kyautata zaton ‘yan bindiga ne suka kashe a wasu kauyuka biyu na gundumar Gandi da ke karamar hukumar Rabbah ta jihar Sokoto cikin mako guda.
Wata majiya da ta zanta da jaridar Punch daga daya daga cikin kauyukan da lamarin ya shafa, ta tabbatar da cewa hare-haren da aka kaddamar a Gidan-Buwai da Maikujera da ke cikin karamar hukumar sun kuma yi sanadiyyar sace dabbobi sama da 300.
Hare-haren mabambanta sun faru ne a cikin al’ummomin biyu cikin kasa da mako guda
Majiyar wacce ya bayyana sunansa Salisu Gandi ta ce ‘yan bindigar da suka kai hari kauyen Gidan–Buwai sun isa kauyen ne a ranar Litinin da daddare.
“Sun kuma yi awon gaba da shanu sama da 100, tumaki 200, da awaki na ’yan uwa da kuma wasu mazauna yankin a cikin lamarin,” in ji shi.
Gandi ya ci gaba da bayanin cewa ‘yan ta’addan da ke kan babura sama da 100 sun isa kauyen na Gidan-Buwai da muggan makamai inda nan take suka fara harbin kan mai uwa da wabi tare da raunata wasu mutanen.
Ya bayyana harin a matsayin mafi muni ganin yadda ‘yan fashin suka kona gidaje da dama, sama da bukka 60, babura 10, da motoci biyar, yayin da mutane bakwai suka samu raunuka daban-daban.
A cewarsa, barayin sun kuma yi awon gaba da kayan shaguna da dama tare da sace kayayyakin masarufi da kayan abinci.
‘Yan bindigar sun kuma yi farautar ‘yan banga a kauyukan inda suka tsananta bincike gida-gida don nemo ‘yan banga.
Sai dai a kwanakin baya ‘yan bindigar sun kai hari kauyen Maikujera inda suka kashe mutane biyar yayin da mutane da dama suka samu raunuka daban-daban.
An kwantar da wadanda suka jikkata a asibitin koyarwa na Jami’ar Usmanu Danfodiyo.
Da aka tuntubi kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, ASP Ahmad Rufa’i, ya tabbatar da faruwar lamarin, amma ya ki cewa komai kan alkaluman.
Ya kuma bai wa mazauna yankin tabbacin cewa rundunar ‘yan sanda za ta sanar da jama’a sakamakon binciken su da zarar sun kammala binciken.
A wani labarin makamancin haka, an kuma samu rahoton wani harin da aka kai a safiyar Larabar nan a kauyen Maikara da ke karamar hukumar Kware a jihar ta Sokoto.
Daya daga cikin mazauna kauyen da ya zanta da wakilinmu da ya nemi a sakaya sunansa ya ce ‘yan bindigar sun kashe mutane biyu, uba daya da dansa a harin.
Ya kuma bayyana cewa ‘yan bindigar sun yi garkuwa da mutane biyar a yayin farmakin da ya ce an kwashe kusan sa’o’i biyu ana yi.
