Addini
Wasu Jihohin Najeriya Sun Ware Sama Da Biliyan 20 Domin Ciyar Da Marasa Galihu A Ramadana
Wasu jihohin arewacin Kasar nan 7 sun sanar da ware kuadden da yawansu ya kai naira biliyan 28 da dubu 300 don ciyar da al’ummominsu a lokacin Azumin watan Ramadana.
A wani yunkuri na saukakawa jama’a matsin rayuwa da tsadar kayakin da ake fama da shi a sassan kasar.
Jihohin kamar yadda jaridar Daily Trust ta rawaito sun kunshi Kano da Katsina da kuma Sokoto sai Jigawa da Kebbi da Niger da kuma Yobe, wadanda suka gabatar da wani tsarin ciyarwa ga marasa galihu don tallafa musu.
Kusan galibin jihohin a cewar jaridar basu bayyana ainahin yawan kudaden da za su yi amfani da su wajen aikin ciyarwar ba, said ai a jumlace kiyasi na nuna yiwuwar kudaden su tasamma biliyan 29.
