Connect with us

Featured

Wasu ‘Yan Bindiga Sun Hallaka Malamin Jami’a Tare Da Sace Wasu Mutane

Ana zargin wasu ‘yan bindiga 8 sanye da bakaken kaya sun kai hari Ajadeh Event Centre da ke Iperu Remo daura da hanyar Sagamu, inda suka kashe wani malamin Jami’ar Babcock Ilisan Remo mai suna Yinka Olowojobi yayin da aka yi awon gaba da wasu guda biyu a yayin harin.

Wata sanarwa da kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Ogun, Omolola Odutola, ya fitar a ranar Litinin, ta ce lamarin ya faru ne a ranar Juma’a, 19 ga watan Afrilu da misalin karfe 9:20 na dare.

An ce ‘yan bindigar sun harbi Olowojobi a kirji bayan sun yin awon gaba da su.

Malamin jami’ar Babcock da aka kashe tare da wani Dare da kuma wani mutum da har yanzu ba a tantance ba da wadanda aka sace an ce suna cikin shakatawa a dakin taro yayin da wadannan gungun ‘yan banga suka kai hari.

Odutola, ya ce ‘yan sanda sun kama wani Awada Ishaya daga jihar Filato a matsayin wanda ake zargi da aikata laifin.

An ce an dauki Ishaya aiki ne makonni biyu da suka gabata a matsayin mai gadi lokacin da aka bude wurin taron.

“Rahoto daga sashin Iperu ya nuna cewa an yi garkuwa da mutane da kuma kisan kai a ranar 19 ga watan Afrilu, 2024, da misalin karfe 9:20 na dare.

“An ruwaito cewa an ji karar harbe-harbe a Ajadeh Event Centre da ke kan titin Sagamu a yankin Iperu a jihar Ogun.

“Shaidun gani da ido sun iya kirga wasu mutane takwas sanye da bakaken kaya dauke da bindigu sun fito daga wani wuri da ba a san ko su waye ba a cikin dakin shakatawa da suka bude wuta ba kakkautawa, inda daga bisani aka harbe wani mutum daya malami a jami’ar Babcock mai suna Olowojobi Yinka a kirji.

“Wani lamari mai kama da zato ya sa ‘yan sanda suka kama wani Awada Ishaya dan jihar Filato wanda aka dauka aiki makonni biyu da suka gabata lokacin da aka kaddamar da cibiyar taron a matsayin jami’in tsaro don ci gaba da yi masa tambayoyi.

“An kai malamin asibitin koyarwa na Jami’ar Babcock, inda aka tabbatar da mutuwarsa.

“Ana nan ana kokarin kamo masu laifin tare da kubutar da wadanda aka sace. Za a yi Karin bayani a nan gaba. “

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişGrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetBetwoonRadissonbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet