Featured
Wasu masu zanga-zanga sun yi dafifi a hedikwatar Jam’iyyar APC, suna neman shugabanta na kasa Abdullahi Ganduje ya sauka daga mukaminsa
Wasu masu zanga-zanga sun yi dafifi a hedikwatar Jam’iyyar APC mai mulki da ke Abuja, suna neman shugabanta na kasa, Abdullahi Ganduje, ya sauka daga mukaminsa.
Masu zanga-zangar suna kuma kira ga Shugaba Bola Tinubu da Sakataren Gwamnati, George Akume, su duba yiwuwar mayar da shugabancin jam’iyyar yankin Arewa ta Tsakiya.
Suna neman Ganduje ya sauka ne kwanaki biyu bayan shugabannin APC na jihohi sun jaddaga goyon bayansu da amincewa ga shugabancinsa.
Gwamnatin Kano Na Kashe Biliyan 1.2 A Duk Wata Don Samar Da Ruwan Sha – Kwamishinan Ruwa
Aminiya ta ruwaito cewa daga cikin masu zanga-zangar, akwai masu dauke da kwalaye da ke dauke da rubutun neman murabus din Ganduje, da masu neman shugabancin jam’iyyar ya koma yankin Arewa a Tsakiya idan ya sauka.
Suna wannan kiraye-kiraye ne bayan dambarwar dakatar da Ganduje da wani tsagin shugabannin mazabarsa da ke Karamar Hukumar Dawakin Tofa a Jihar Kano suka dakatar da shi.
Yansanda A Jihar Bauchi Sun Kashe Masu Garkuwa Da Mutane 8, Sun Kubutar Da Mutane 3
Sun sanar da dakatar da shi ne kan zargin da almundahar kudade da cin rashawa a lokacin da yake gwamnan jihar da gwamnatin jihar mai ce ke masa.
Sai dai daga bisani wani tsagin shugabanincin mazabar ya yi watsi da su, lamarin da ya kai su kotu kuma kotu ta amince da dakatarwar.
Sai dai daga bisani kotun ta janye dakatarwar, kuma har yanzu ƙurar bata lafa ba.
