Connect with us

Featured

Ina addu’ar Allah ya fahimtar dani addinin Musulunci – Jaruma Tonto Dikeh

Fitacciyar jaruma a masana’antar shirya fina finai ta kudancin Najeriya, Tonto Dikeh ta ce babbar addu’ar ta shi ne ta fahimci addinin Musulunci.

Jarumar ta bayyana sha’awar ta ga addinin ne a wani sako da ta wallafa a shafin Instagram .

Ta ce kiran Sallah daga Masallacin da take makotaka da shi na tashinta daga bacci tsawon shekaru 4 inda ta bayyana kiran Sallah a matsayin “Sauti na soyayya da sadaukarwa inda ake ambaton ubangiji”.

Dikeh ta kuma nemi sanin ko akwai wata hanya da za a dinga bada tallafi ga Masallaci baya ga tallafin kudi.

” Sauti mai dadi na tashi na a kullum tsawon shekaru 4. Sauti ne na soyayya da sadaukarwa, sauti na ubangiji”, kamar yadda ta wallafa.

“Idan ina son bada tallafi ga Masallaci, mai zan iya bayarwa bayan kudin? Allah ya albarkaci dukkan Musulmi, ina sauraron addu’o’in ku, Allah ya amsa muku.

Ta kuma yaba wa Musulmi wajen sadaukarwarsu da riko da addininsu.

” Babbar addu’a ta ita ce na fahimci addinin Musulunci”, inji ta.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişGrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetBetwoonRadissonbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet