Featured
Majalisar Wakilai ta dakatar da gwamnatin tarayya daga aiwatar da yarjejeniyar Samoa
Majalisar ta kuma ce za ta binciki yarjejeniyar wacce gwamnatin tarayya ta sanyawa hannu a ranar 28 ga watan Yuni.
Majalisar ta amince da hakan ne bayan kudurin gaggawa da dan majalisa mai wakiltar Dala, Ali Sani Madakin Gini ya gabatar tare da hadin gwiwa da ‘yan majalisu 87.
Batun yarjejeniyar dai ya haifar da ce-ce-ku-ce a Najeriya bisa zargin tana kunshe da ‘yancin masu auren jinsi.
