Featured
Hajji 2024: An kammala jigilar dawo da Alhazan jihar Kano gida
Jirgin karshe dake dauke da Alhazan jihar Kano ya baro birnin Jeddah zuwa Kano wanda hakan ya kawo karshen kammala aikin Hajjin bana.
Jirgin na Max Air ya bar kasar ta Saudia ne da misalin karfe 12 na dare inda ya sauka a Kano da karfe 4:26 dauke da Alhazai 404 daga kananan hukumomi 3.
Bayanin hakan na dauke ne cikin wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na hukumar jindadin Alhazai ta jihar Kano, Sulaiman A Dederi ya fitar a yau Laraba.
Darakta janar na hukumar jindadin Alhazan na jihar Kano, Alhaji Lamin Rabiu Danbappa ya bayyana godiyarsa ga masu ruwa da tsaki da suka hada hukumomin Saudia da kafanunuwan jiragen sama bisa goyan bayan da suka bayar.
“Mun yi farin ciki Alhazanmu sun kammala aikin Hajji cikin nasara kuma mun dawo gida lafiya kalau”, inji shi.
