Featured
Abba Ya Nada Sabbin Sarakuna Uku A Kano
A cikin daren jiya Talata Gwamna Abba Kabir Yusuf ya mika takardun fara aiki ga sabbin sarakunan masarautun Gaya da Karaye da kuma Rano.
Sabbin sarakunan su ne Alhaji Muhammad Maharaz Karaye, a matsayin Sarkin Karaye, wanda kafin yanzu shi ne Hakimin Rogo.
Sai Hakimin Bunkure, Alhaji Muhammad Isa Umar, a matsayin sabon Sarkin Rano.
Na uku shi ne Sarkin Gaya, Alhaji Aliyu Ibrahim Abdulkadir, wanda gwamnatin jihar ta tsige a watan Mayu tare da takwarorinsa na masarautun Bichi da Rano da Kano da kuma Karaye da aka rushe.
Gwamnan ya kuma umarci sarakunan masu daraja ta biyu da su kasance masu wanzar da zaman lafiya da hadin kan al’umma da kuma raya al’adu.
