Featured
Matsin Tattalin Arziki: Gwamnatin APC ta gaza – Gwamnonin PDP
Kungiyar gwamnonin jam’iyyar PDP ta bayyana damuwa kan yadda gwamnatin tarayya karkashin jagorancin APC ke tafikar da tattalin arzikin kasarnan.
A sanarwar da gwamnonin suka fitar bayan kammala taronsh a Enugu a jiya Laraba sun yi Alla-wadai da manufofin gwamnatin tarayya kan tattalin arziki wanda suka ce sun jefa ‘yan Najeriya cikin mawuyacin hali.
Shugaban kungiyar kuma gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed ne ya gabatar da takardar bayan taron da ya shafe awanni 4 ana yinsa.
Gwamnonin sun kuma ayyana goyan bayansu ga kungiyar kwadago ta NLC kan batun mafi karancin albashi.
Bala Muhammad ya ce bayan doguwar tattaunawa, kungiyar gwamnonin PDP “sun nuna damuwarsu kan yadda gwamnatin tarayya karkashin APC ke tafiyar da lamuran tattalin arziki”.
Gwamnonin sun bukaci shugaba Tinubu ya dau matakan dawo da martabar kasar nan.
