Featured
Yanzu-Yanzu: Tinubu ya sanya hannu kan dokar kafa hukumar raya yankin Arewa maso yamma
Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya sanya hannu kan kudurin dokar kafa hukumar raya yankin Arewa maso yamma.
Barau Jibrin, mataimakin shugaban majalisar dattawa ne ya bayyana hakan yayin ganawa da manema labarai a birnin tarayya Abuja a yau Talata.
Sanata Barau, wanda shi ne ya dauki nauyin kudurin dokar kafa hukumar, ya bayyana farin cikinsa ga yadda shugaban kasar ya nuna damuwa kan kalubalen da al’ummar yankin Arewa maso yamma ke fuskanta.
Barau ya ce “Shugaban kasa ya sanya hannu kan kudurin dokar kafa hukumar raya yankin Arewa maso yamma. Kuma hukuma ce da za ta tallafawa ci gaban yankin.”
