Featured
Fiye da yan Najeriya miliyan ɗaya ne ke fama da matsananciyar yunwa – Bankin Duniya
Wani rahoto da Bankin Duniya Ya fitar yace Najeriya na fuskantar matsalar ƙarancin abinci, inda sama da mutane miliyan ɗaya ke fuskantar matsalar a shekarar 2024, idan aka kwatanta da na shekarar da ta gabata.
Sabon rahoton da aka fitar baya bayan nan ya nuna cewa ƙasashe kamar Najeriya, Habasha da Yemen, sun sami ƙaruwa sosai a yawan mutanen da ke fuskantar matsalar ƙarancin abinci.
Tun bayan da shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya shiga ofis a watan Mayu, ya aiwatar da sauye-sauyen tattalin arziki wanda da suka jefa wasu ƴan ƙasar cikin mawuyacin hali.
Sai de kuma rahotan ya nuna cewa, wasu ƙasashe kamar Afghanistan da Kenya sun samu raguwar
Ƙasashe irin su Afghanistan da Kenya kuwa an ba da rahoton raguwar karancin rashin abinci.
