Featured
Shugaba Tinubu ya rantsar da sabbin ministocinsa
Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu, ya rantsar da sabbin ministocinsa da ya nada su.
shugaban , ya rantsar da sabbin ministocin ne yau Litinin a fadar mulki ta Aso Villa da ke birnin tarayya Abuja.
A jawabinsa jim kaɗan bayan rantsar da ministocin, shugaba Bola Tinubu, ya ce, ya dauki matakin nadin nasu ne a kokarinsa na farfado da tattalin arzikin Najeriya tare da cewaya na kan kan tafarki mai kyau domin cika burinsa na samar da ci gaba ga ‘ya’ya da jikokin al’ummar Najeriya.
Karanta: Kano APC Crisis: An Open Letter to President Tinubu
Haka kuma, ya ce, ana ci gaba da aikin inganta tattalin arzikin ƙasa domin magance kalubalen da ake fuskanta.
Shugaba Tinubu, ya bayyana wa sabbin ministocin cewa ya zabo su ne domin su bayar da gudunmuwarsu wajen ceto Najeriya.
BBC ta ruwaito cewa, A ranar 30 ga watan jiya na Oktoba ne Majalisar Dattawa ta tantance tare da amincewa da sabbin ministocin wadanda suka hadar da Ministan jinƙai da rage talauci Dr Nentawe Yilwatda da inistan ƙwadago, Muhammadu Maigari Dingyadi da ƙaramar ministar harkokin waje, Bianca Odumegwu-Ojukwu.
Sai kuma Ministan masana’antau da kasuwanci da zuba jari, Dr Jumoke Oduwole da ministan kula da dabbobi, Idi Mukhtar Maiha da ƙaramin minstan gidaje, Yusuf Abdullahi Ata da ƙaramar ministar ilimi, Dr Suwaiba Said Ahmad.
