Featured
Za mu cigaba da bibiyar lamarin harin Tudun Biri, har sai waɗanda suke da hannu sun fuskanci hukunci – Uba Sani
Gwamnan Jihar Kaduna Sanata Uba Sani, ya kaddamar da cibiyar kula da lafiya mai gadaje 25, da cibiyar koyar da sana’o’i, a karamar hukumar Tudun Biri da ke jihar, domin cika shekara guda da wani jirgi mara matuki ya kai hari a yankin.
Gwamnan ya kuma raba buhu 300 na shinkafa 50kg, da buhunan masara 300, da takin NPK buhu 500 ga al’ummar yankin da kauyukan da ke kewaye.
Idan za’a iya tunawa tun a daren ranar Laraba 3ga Disamba, 2023, sama da mutane 80 ne suka rasa ransu, lokacin da wani jirgin yaki mara matuki na Sojoji ya kaiwa mutanen kauyen hari da kuskure a wajen bikin Mauludi.
Gwamna Uba Sani ya jagoranci tawagar gwamnati bayan faruwar lamarin, inda ya yi alkawarin samar da ababen more rayuwa, kamar tituna, ruwa, makaranta, asibiti da cibiyar koyar da sana’o’i ga al’umma.
A jiya Lahadi 01 ga Disamba, Gwamnan ya kaddamar da cibiyar kula da lafiya a matakin farko mai gadaje 25 tare da motar daukar marasa lafiya, da Cibiyar Samar da Fasaha.
Ya yi tabbatar da cewa za a bayar da jarin ga wadanda sukansamu kwarewa a bangaren koyon sana’o’i.
A karshe gwamnan yayi alkawari ga mazauna yankin wadanda suka rasa yan uwan su yayin harin, cewa gwamnatin Kaduna za ta cigaba da bibiyar lamarin, har sai wadanda suke da hannu kan lamarin sun fuskanci hukuncin da ya dace da su.
