Connect with us

Featured

Jam’iyyar PDP Ta Gudanar Da Taron Warware Rikicin Cikin Gida

Kwamitin gudanarwa na babbar jam’iyar hammaya a Najeriya wato PDP ya gudanar da wani taro a birnin Abuja, don duba matsalolin da jam’iyyar ke fama da su.

Kafofin yaɗa labaran cikin gida sun ce wannan shi ne karon farko da kwamitin ya yi taro ƙarƙashin jagorancin shugaban jam’iyyar na riƙo Ambasada Umar Damagun a bana.

Gabanin taron dai an so a samu yamutsi, inda tarin ƴan daba ɗauke da makamai suka mamaye ƙofar shiga shalkwatar jam’iyyar da ke Wadata Plaza a Abuja, kafin daga baya jami’an tsaro suka tarwatsa su.

Majalissar Dattawa Ta Mayar Da Martani Kan Korafin Sanata Natasha

Taron na zuwa ne bayan da kotun ƙoli ta yi watsi da buƙatar dakatar da aiwatar da hukuncin da wata babbar kotu ta yanke na tsige Sanata Samuel Anyanwu daga mukamin sakataren jam’iyyar na ƙasa, inda ta maye gurbinsa da Hon Sunday Udeh Okoye.

Malam Ibrahim Abdullahi, mataimakin sakataren watsa labarai na jam’iyyar ta PDP a Najeriya ya shaidawa BBC cewa taron ya tattauna akan batutuwa da dama ciki harda matsalolin jam’iyyar na baya baya nan:

”Taro ne wanda ya shafi matsalolin jam’iyya musaman na baya baya nan waɗanda suke da alaƙa da matsayin kwamitin amintattu, don a yi mu su tuni cewa kujerun wasunsu ya riga ya kai ƙarshen wa’adi da kuma abubuwan da suka shafi ofishin shugaban jam’iyya watau sakataren jam’iyya na ƙasa ”

”Taron ya kuma yi nazari kan inda jam’iyyar ta kwana a yanzu, matsayin matsalolin da ke ƙasa duk sune aka tattaunawa don a samu shawarwarin yadda za a ciyar da ita gaba’,’ in ji shi.

Game da rikicin sakataren jam’iyyar kuwa, Malam Ibrahim ya ce kamata ya yi a yi hakuri a jira hukuncin kotu

Share this:
meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişGrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetDeneme Bonusu Veren SitelerCratosroyalbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasinolevantjojobetgrandpashabetmarsbahismarsbahismarsbahisjojobetjojobetjojobetjojobet girişmarsbahisjojobetgrandpashabetholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabet girişjojobetjojobetgrandpashabetsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahisjojobetjojobetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet