Featured
Majalissar Dattawa Ta Mayar Da Martani Kan Korafin Sanata Natasha
Malisar Dattawan Kasar nan ta mayar da martani kan koken da Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan ta gabatar a gaban Kungiyar Majalisun Kasashen Duniya (IPU) ta Majalisar Dinkin Duniya ta hanyar wata wasika da Shugaban Masu Rinjaye na Majlisar Dattawan Kasar Sanata Opeyemi Bamidele ya rubuta wa IPU ɗin.
Wasikar da ’yar majalisar wakilai Kafilat Ogbara wadda take wakiltar Nijeriya a IPU ta karanta ta ce an dakatar da Natasha ne saboda laifin rashin ɗa’a, ba domin zargin cin zarafi ba.
Tinubu Ya Jaddada Muhimmancin Bin Doka Don Tabbatar Da ɗorewar Zaman Lafiya
Majalisar dattawan ta bukaci jama’a da su yi watsi da labaran kanzon kurage da wasu kafafen yada labarai suke yadawa dangane da batun dakatar da ’yar majalisar dattawan tsawon wata shida.
