Connect with us

Featured

Ana Zargin Wasu ‘Yan Gida Daya Da Yi Wa Almajiri Yankan Rago A Adamawa

Rundunar ’yan sandan jihar Adamawa ta cafke wani ƙani da yayansa mai suna Aliyu Abdulmalik da Ibrahim Abdulmalik bisa zargin yanke kan wani almajiri ɗan shekara 10, Abdallah Lawali.

Bayanai sun ce ’yan uwan junan biyu sun aikata wannan ta’asa ne a ranar 7 ga watan Maris a unguwar Sarkin Yamma da ke Ƙaramar Hukumar Jada.

Sanarwar da rundunar ’yan sandan ta fitar ta ce an kama ababen zargin ne da gangar jikin almajirin a cikin wani buhu, yayin da aka ƙwaƙulo kansa a cikin wani rami da suka binne a harabar gidansu.

Rundunar wadda ta ce yanzu haka bincike ya kankama a kan lamarin, ta kuma bayyana cewa ababen zargin sun yi iƙirarin aikata laifin da suka alaƙanta da sharrin shaiɗan.

Kwamishinan ’yan sandan jihar CP Dankombo Morris, ya tabbatar da cewa za a yi adalci a lamarin, yayin da yake kira ga al’umma da su kasance masu lura da miƙa rahoton duk wani motsi da su aminta da shi ba zuwa ofishin mahukunta mafi kusa.

Share this:
meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftdinamobetgrandpashabet girişgrandpashabetdinamobetGrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetDeneme Bonusu Veren SitelerCasibomcasino sitelerikavbettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasinolevantcasinolevantcasinolevantcasinolevantholiganbetjojobetgrandpashabetgrandpashabetsahabetsahabetonwinonwinmarsbahisjojobetjojobetjojobetjojobetjojobetjojobetgrandpashabetgrandpashabetholiganbettipobetsekabetsekabetholiganbetsahabetsahabetcasibomcasinolevantbetgarantibetciograndpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahissekabetgrandpashabetjojobetpusulabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabetGrandpashabet